11 Satumba 2021 - 11:53
​Rasha: Ba Za Mu Goyi Bayan IAEA Domin Takura Wa Iran Ba

Gwamnatin kasar Rasha ta ce ba za ta goyi bayan duk wani mataki da hukumar IAEA za ta dauka domin takura wa kasar Iran ba.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : ta bayar da rahoton cewa, wakilin kasar Rasha a hukumar kula da makashin nukiliya ta duniya Mikhail Ulyanov ya sanar da cewa, kasarsa ba za ta goyi bayan duk wani mataki da hukumar IAEA za ta dauka a kan kasar Iran ba.

Uyanov ya ce babu wani dalili da zai sanya hukumar ta siyasantar da ayyukanta, domin kuwa irin bayannan da ta bayar dangane da shirin Iran na nukiliya a baya-bayan nan ba mu taimakawa ba ne wajen warware takaddamar shirin Iran na nukilya.

A kan haka ya ce, a zaman da alkalan hukumar za su gudanar, idan har suka fitar da wani kudiri na daukar matakan takurawa kasar Iran, to a nan take Rasha za ta yi fatali da shi, kuma za ta hana kudirin wucewa.

A cikin rahoton baya-bayan nan da hukumar makamashin nukiliya ta duniya ta bayar kan shirin Iran na nukiliya, ta ambaci wasu abubuwa da za su iya sanya shakku kan shirin na Iran, wanda kasashen turai ke zargin cewa Iran tana kera makaman kare dangi ne, wanda suke kallon hakan a matsayin babbar barazana a gare su, zargin da kasar ta Iran take musuntawa.

342/